Fadar shugaban kasa ta nesanta shugaban kasa, Muhammadu Buhari, daga shirin bai wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan damar ya gaje shi a 2023.
A zantawarsa da Daily Independent, wani babban hadimin shugaban kasa ya ce, shugaban kasar ba ya bayan yunkurin janyo Jonathan cikin jam’iyyar APC mai mulki da kuma mayar da shi dan takarar jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023.
Ya bayyana cewa, shugaba Buhari ba zai taba barin Jonathan ya gaje shi ba, bayan da ya yi kakkausar suka a kan yadda ya karkata akalar arzikin kasar nan a lokacin da ya shafe shekaru hudu yana mulki.
Sai dai mai taimaka wa shugaban kasa, ya ce, Buhari na matukar mutunta Jonathan kan yadda ya amince da sakamakon zaben shugaban kasa na 2015 da kuma tursasa matsin lamba daga wasu magoya bayansa na kin amincewa da zaben.