Rundunar ƴan sanda a jihar Imo ta tabbatar da mutuwar wani jami’inta Cosmos Ugwu sakamakon harbin da budurwarsa ta yi masa.
Budurwar ta harbi Ugwu ranar Talatar da ta gabata. Hukumomi sun bayyana sunanta da Amanda Uchechi Ugo, ƴar asalin ƙaramar hukumar Ahiazu Mbaise wadda shekarunta 23.
Jaridar Punch ta ruwaito daga majiyoyi masu tushe cewa lamarin ya faru a ofishin rundunar da ke Ezinihitte da yammacin ranar rabon kyaututtuka da ake kira Boxing Day a Turancin Ingilishi.
Jami’an da ke aiki a ranar sun ce sun ji harbin bindiga sau uku daga ɗakin marigayin.
“Lokacin da ƴan sanda suka garzaya zuwa ɗakin domin ganin abin da ke faruwa, sai suka ga jami’in mai muƙamin kofur kwance cikin jini.
Wata majiya ta shaida wa jaridar The Punch cewa matashiyar ta harbe shi sau uku a ƙirji da kuma hannunsa na hagu. An garzaya da shi asibitin Evergreen a Ezinihitte, inda likita ya tabbatar ya mutu.”
A yanzu dai matar da ake zargi tana hannun ƴan sanda domin amsa tambayoyi da kuma yiwuwar gurfanarwa a kotu.
Da aka tuntuɓe shi, kakakin rundunar ƴan sanda ta jihar Imo, Henry Okoye ya tabbatar da faruwar al’amarin inda ya ce ƴan sanda suna duk mai yiwuwa domin duba abin da ya faru.


