Kungiyar manoman shinkafa ta ce, sake bude kan iyakar Najeriya da Nijar ne ya janyo faduwar farashin shinkafa a fadin kasar.
Jonathan Joshua, shugaban kungiyar African Rice Millers da ke Nasarawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.
Joshua, wanda ya zama shugaban kungiyar masu noman kanana a Najeriya na kasa, ya bayyana cewa ana sa ran farashin shinkafa zai kara faduwa nan da watanni biyu masu zuwa da fara noman.
“Wasu masana’antun da suka dakatar da noman su saboda karancin paddy a shekarar da ta gabata da farkon wannan shekarar a yanzu haka suna sake budewa saboda suna iya samun hatsi cikin gaggawa daga kasashen makwabta saboda sake bude kan iyakar Najeriya da Nijar.
“Muna sa ran farashin paddy zai kara raguwa lokacin da manoma suka fara girbi cikin watanni biyu,” in ji shi.
Farashin shinkafa ya ragu da kashi 19 cikin dari duk da hauhawar farashin kayayyaki wanda ya kai kashi 33.20 cikin 100 a watan Maris din 2024.