Ɗan wasan tsakiyar Manchester United Bruno Fernandes ya tsawaita zamansa a ƙungiyar da shekara ɗaya.
Ɗan ƙwallon mai shekara 27 wanda ya koma ƙungiyar a Janairun 2020 kan kuɗi fan miliyan 47 biyan farko, yanzu yana kan yarjejeniya zuwa 2026 kuma wannan kwantaragin na da zaɓin tsawaita shi da shekara ɗaya.
Fernandes ya ci wa United ƙwallo 49 a wasa 117 a dukkan gasanni. Kazalika, ya bayar an ci ƙwallo 39.
“Ina son cimma ƙarin wasu abubuwan da yawa a nan, kuma haka su ma sauran ma’aikata da ‘yan wasan,” a cewarsa.