Kyaftin din Manchester United, Bruno Fernandes, ya yi gargadi ga Manchester City, Arsenal, Chelsea, Liverpool da sauran masu neman lashe kofi a bana, yana mai shan alwashin cewa, Ƙungiyar sa za su yi yaki da kowane don lashe kofi a kakar wasa ta bana.
Dan wasan na Portugal ya yi wannan gargadin ne bayan Manchester United ta doke Arsenal da ci 2-0 a wasan sada zumunta da suka yi ranar Asabar.
United ta doke Leeds United da Olympique Lyon da ci 2-0 da kuma 1-0, a wasannin da suka gabata a wasannin share fage kafin tashi zuwa Amurka.
Tawagar Erik ten Hag ta ci gaba da taka rawar gani a kasar Amurka, inda ta samu nasara kan Arsenal da ci 2-0 a filin wasa na MetLife.
Fernandes ya bayyana ra’ayinsa na ganin kungiyar ta fafata domin lashe kowacce gasa hudu da take shiga.
“Muna son yin gwagwarmaya don samun lakabi,” in ji Fernandes ta hanyar football.london.
“Muna so mu je daukar dukkan kofunan da muke ciki. Na fadi hakan tun lokacin da na zo kulob din – ko da a cikin mafi munin lokaci.
“Muna so mu tafi don duk abin da muke ciki kuma kocin ya sanar da kowa cewa wannan shine ka’idodin kulob din, abin da kulob din ya cancanta, abin da ya kamata mu tsara wa kanmu don zama dan wasan Man Utd.”