Birtaniya da Australia sun bukaci ‘yan kasarsu su guji zuwa Najeriya saboda dalilai na tsaro.
A cikin wani sakon shawarwari kan tafiye-tafiye, gwamnatin Australia ta bukaci janye duk wani shiri ko tunanin zuwa Najeriya ga ‘yan kasarta saboda ana shirin gudanar da manyan zabuka a kasar, kuma akwai fargabar da ake ta barkewar tashe-tashen hankula da ke da nasaba da zabe.
Cikin sakon, gwamantin ta Australia ta ce akwai zargin hare haren da ake kitsawa na kai hari kan ofisoshin hukumar zabe, don haka kasar ta shawarci ‘yan kasarta da su nisanta kansu da zuwa Najeriya.
Itama gwamnatin Birtaniya ta yi gargadin cewa za a iya samun barkewar zanga-zanga a lokacin zabe, don haka ne ta shawarci ‘yan kasarta da zaune a Najeriyar da ma wadanda ke shirin zuwa kasar da su guji zuwa Najeriya musamman a wannan lokaci da zabuka ke tafe a Najeriya.
Kazalika itama kungiyar Tarayyar Turai, ta yi gargadin cewa rashin tsaro na iya hana a gudanar da zabe a wasu sassan kasar ta Najeriya.
Da take mayar da martani kan damuwar da wadannan kasashe suka nuna, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce kasar na cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya har zuwa lokacin zabe, inda ta kara da cewa ba wannan ne karon farko da kasashen ketare ke fitar da sanarwar mai kama da wannan ba ga ‘yan kasarsu.
A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne dai kasashen Amurka da Birtaniya da Canada da Jamus da Bulgeriya suka fitar da sanarwar kan ta’addanci, inda suka gargadi ‘yan kasarsu a Najeriya da su guji manyan shagunan siyar da kayayyaki da wuraren ibada da otal-otal da suka ce ‘yan ta’adda za su iya kai wa hari.
Sai dai Gwamnatin Tarayyar kasar ta yi watsi da wannan gargadi, inda ta bayyana su a matsayin na karya, ta kuma ba ‘yan Najeriya tabbacin gudanar da harkokinsu bisa doka domin kasar na cikin kwanciyar hankali.