Shafin sada zumunta na X, ya ce, yana sa ran za a toshe dandalin a Brazil bayan kasa cika wa’adin da aka bai wa kamfanin na gabatar da sabon lauya.
A cikin wata sanarwa, kamfanin X ya bayyana ƙarara cewa bai bi umarnin ba, wanda alkalin Kotun Kolin Brazil ya bayar a ranar Laraba.
A ci gaba da shari’ar da ake yi da kamfanin, alkalin Kotun Kolin Brazil ya zargi kamfanin X da yaɗa bayanan ƙarya.
Mamallakin shafin, Elon Musk, ya ce yunƙurin toshe shafin a Brazil, wani ƙoƙari ne na hana yin rawar gaban hantsi a dandalin. Tuni dai X ya rufe ofisoshinsa a Brazil.
Tun da farko Elon Musk ya ce, zai ba masu amfani da dandalin nasa intanet kyauta har zuwa lokacin da za a warware taƙaddamar.