fidelitybank

Brazil ta ci tarar ɗan wasa Neymar

Date:

Mahukuntan kula da gine-gine a Brazil sun ci tarar Neymar, bayan da karo biyu yana kin bin umarni dakatar da wasu gine-gine da yake yi a gidansa.

Tsohon dan kwallon Barcelona yana da katafaren gida mai dauke da kayayyakin alfarma da kawa a Rio de Janeiro.

Tun farko dan kwallon tawagar Brazil da Paris St Germain na fuskantar biyan wata tarar da kai fam miliyan daya.

Hakan ya biyo bayan da mahukuntan suka ce sun gano Neymar yana gina wani kududdufin yin waka da wani tsibiri a gefensa a garin Mangaratiba.

Mahukuntan sun dakatar da ci gaba da aikin, inda wasu kafar yada labarai a Brazil suka ce sai dan kwallon ya gayyaci mutane biki da wanda a kududdufin.

Ranar Asabar mahukuntan suka kara kai ziyara gidan Neymar suka ga yadda aka yi biris da umarnin da suka bayar tun farko kan a dakatar da aika-aikace.

Wakilan Neymar har yanzu ba su ce komai ba, bayan da kamfanin dillacin labarai na AFP ya tuntube su.

Neymar mai shekara 31, yana jinya bayan da likitoci suka yi masa aiki a kafarsa ta hagu tun a watan Maris a Doha a Qatar.

Rabon da dan wasan ya taka leda tun cikin watan Fabrairu, har ma ana ta rade-radin cewar da-kyar idan zai iya ci gaba da taka leda a PSG a kakar da za a fara.

Neymar ya sayi katafaren gidan da ke garin Mangaratiba a 2016, wanda ke dauke da gine-ginen alfarma da kaya na kawa.

national news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp