Tsohon dan kwallon Barcelona yana da katafaren gida mai dauke da kayayyakin alfarma da kawa a Rio de Janeiro.
Tun farko dan kwallon tawagar Brazil da Paris St Germain na fuskantar biyan wata tarar da kai fam miliyan daya.
Hakan ya biyo bayan da mahukuntan suka ce sun gano Neymar yana gina wani kududdufin yin waka da wani tsibiri a gefensa a garin Mangaratiba.
Mahukuntan sun dakatar da ci gaba da aikin, inda wasu kafar yada labarai a Brazil suka ce sai dan kwallon ya gayyaci mutane biki da wanda a kududdufin.
Ranar Asabar mahukuntan suka kara kai ziyara gidan Neymar suka ga yadda aka yi biris da umarnin da suka bayar tun farko kan a dakatar da aika-aikace.
Wakilan Neymar har yanzu ba su ce komai ba, bayan da kamfanin dillacin labarai na AFP ya tuntube su.
Neymar mai shekara 31, yana jinya bayan da likitoci suka yi masa aiki a kafarsa ta hagu tun a watan Maris a Doha a Qatar.
Rabon da dan wasan ya taka leda tun cikin watan Fabrairu, har ma ana ta rade-radin cewar da-kyar idan zai iya ci gaba da taka leda a PSG a kakar da za a fara.
Neymar ya sayi katafaren gidan da ke garin Mangaratiba a 2016, wanda ke dauke da gine-ginen alfarma da kaya na kawa.


