Wani Botoromi ya kashe Malam Usman Maigadi, mai gadi a gona mallakar Sarkin Yauri, Dr Muhammad Zayyanu-Abdullahi.
A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, dabbar ta yi zaton cewa marigayin ya zo ne domin ya cutar da jaririnta, shi ya sa aka kai harin don kare kai.
Marigayin mai shekaru 60 da haihuwa, dabbar ta kai masa hari ne a ranar Lahadin da ta gabata a lokacin da yake kamun kifi a kogin Yauri da ke kauyen Tillo a karamar hukumar Yauri ta jihar.
Shugaban karamar hukumar, Alhaji Abubakar Shu’aibu, ya ce an yi jana’izar Maigadi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garin Yauri, bayan kammala sallar jana’iza.
Har ila yau, Gwamna Nasir Idris, a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Alhaji Ahmed Idris, ya fitar, ya jajanta wa masarautar Yauri da iyalan marigayin.
Idris ya bukaci masarautar da iyalan mamacin da su jajirce wajen karbar nufin Ubangiji cikin aminci.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayin ya kuma saka masa da Jannatul Firdaus.


