Tsohon Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya samu goyon ‘yan majalisa 100 na jam’iyyarsu ta Conservative don sake ɗarewa kujerar, a cewar majiyoyin kamfe ɗinsa.
Adadin ya saɓa wa yawan mutanen da aka sanar na mutum 50 da aka ce su ne ke mara wa Mista Johnson baya, kamar yadda binciken BBC ya nuna.
Rishi Sunak ya sha gaban Johnson a yawan masu goyon baya kuma ana sa ran zai bayyana sha’awar takararsa nan gaba kaɗan.
Penny Mordaunt ce kaɗai ta bayyana takararta a fili ya zuwa yanzu.
‘Yan majalisar na Conservative da ake wa laƙabi da Tory sun musanta nan take rahotannin da ake yaɗawa cewa Mista Johnson ya samu ƙuri’un da yake buƙata na shiga zagayen farko na zaɓen.


 

 
 