Zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Tinubu, zai koma da zama a gidan zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da ke Abuja, babban birnin ƙasar, gabanin bikin rantsar da shi, a cewar tawagar yakin neman zaɓensa.
“Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa zai koma gidan tsaro, a Maitama, inda zai shafe watanni biyu a ciki, daga nan kuma zai koma fadar shugaban ƙasa,” in ji sanarwar a cikin wani sakon Twitter.
Ba a fayyace lokacin da Mista Tinubu zai koma wurin ba.
Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar zai gudanar da muhimman taruka a wurin, kamar yadda wata jaridar ƙasar ta ruwaito.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari mai barin gado ya koma ama a gidan kafin rantsar da shi a watan Mayun 2015.
An ayyana Mista Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da kashi 37%.
Sai dai, ‘yan adawa sun ce za su kalubalanci sakamakon a kotu.
Suna da kwanaki 21 daga ranar da aka bayyana sakamakon zaɓen domin kalubalantar sakamakon a kotun kolin Najeriya.