Tsohon mataimakin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin sadarwa, Bashir Ahmad, ya yi tsokaci kan wanda zai iya zama sabon ministan man fetur.
Ahmad yayi ikirarin cewa Tinubu ne zai iya zama ministan albarkatun man fetur.
Ya yi nuni da cewa, Tinubu ya bi diddigin tsoffin shugabannin kasa, Olusegun Obasanjo da Buhari, wadanda suka zabi baiwa kansu ma’aikatar.
A sakon da ya wallafa ya ce, “Shugaba Bola Tinubu ne babban ministan albarkatun man fetur na mu. Zai bi sahun tsofaffin shugabannin kasa Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari, wadanda suka rike mukamin a zamaninsu.
“A wannan karon akwai kananan ministoci guda biyu a karkashin ma’aikatar, karamin ministan mai da karamin ministan albarkatun iskar gas.”
baiwa kansa ma’aikatar tare da nada Timipre Sylva a matsayin karamin ministan man fetur.
Sai dai kuma shugaba Tinubu ya raba ma’aikatar gida biyu yayin da ya kafa majalisar ministocinsa.