Gwamnatin jihar Borno, ta ce akwai yara kimanin miliyan 1.8 da ba sa zuwa makaranta a fadin jihar sakamakon rikice-rikicen ƙungiyar Boko Haram.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Abba Wakibe na bayyana haka a lokacin bikin ƙaddamar da horo kan wani shiri da gwamnatin jihar ta ɓullo da shi kan fadakarwa game da illar rashin zuwa makaranta.
Ya jaddada cewa, tashe-tashen hankula masu alaƙa da ayyukan ƙungiyar Boko Haram sun shafi ɓangaren ilimi, ciki har da yawan yaran da ke zuwa makaranta.
Ya ƙara da cewa ”muna da marayu 56,000 da zawarawa 49,000, to amma ba su san adadin yawan yaran da ba sa tare da iyayensu”.