fidelitybank

Boko Haram ta sake katse tirken lantarkin da ya hada Damaturu da Maiduguri

Date:

Rahotanni sun ce ‘yan ta’addar Boko Haram sun lalata layin Damaturu-Maiduguri mai karfin Kilovolt 330 bayan makonni uku da dawo da shi.

Wani mai sharhi kan harkokin tsaro Zagazola Makama ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi.

A cewarsa, ‘yan ta’addan sun tarwatsa ma’aikatun TCN da bama-bamai a safiyar ranar Lahadi.

Wannan ci gaban ya jefa Maiduguri da kewaye cikin duhu.

“Maharani sun yi amfani da bama-bamai wajen tarwatsa ginin da misalin karfe biyu na rana, inda suka mayar da Maiduguri da kewaye cikin duhu. Wannan alama ce ta maimaituwa na hare-hare masu mahimmanci daga masu tayar da kayar baya, ”in ji sakon.

Lamarin na zuwa ne makonni bayan da TCN ta maido da layin a ranar 4 ga Satumba, 2024, bayan lalata ta da ‘yan ta’adda suka yi a baya.

A halin da ake ciki, TCN ba ta yi magana a hukumance kan sabon lamarin ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.

bbc news nigeria today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp