Kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno Abdu Umar ya ce, mayakan Boko Haram sun sace wasu mata biyu a kauyen Mairari da ke karamar hukumar Konduga.
Umar ya bayyana haka ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Maiduguri, ya ce, lamarin ya faru ne a ranar 7 ga watan Yuni.
“Da misalin karfe 7:30, wani Ari Mustapha na kauyen Mairari a Konduga, ya ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka mamaye gidansa tare da yin garkuwa da ‘ya’yansa mata guda biyu.
Ya ce suna da shekaru 26 da 30.
“Ya kuma ce maharan sun sace bijimai biyu da wasu kayayyaki kafin su gudu,” in ji kwamishinan.
Umar ya ce rundunar za ta zafafa bincike har sai an kubutar da wadanda lamarin ya rutsa da su, tare da haduwa da iyalansu.
Kwamishinan ya bukaci jama’a da su kai rahoto ga jami’an tsaro na kusa da su.