Ɗaruruwan farar-hula ne ke tserewa muhallansu a wasu garuruwan jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, sakamakon harin da masu iƙirarin jihadi suka kai wani sansanin sojin ƙasar.
Mayakan Boko Haram sun tilasta wa sojoji ficewa daga sansanin bayan kai musu hari a karamar hukumar Marte, tare da hallaka sojoji huɗu da ƙwace makamai kafin daga bisani su ƙona sansanin.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce a baya-bayan nan mayaƙan na Boko Haram sun ɗaiɗiata ɗaruruwan ƙauyuka da munanan hare-hare.
Sai dai duk da hakan hukumomi na cewa mutanen su koma muhallansu, duk da fargabar da ƙungiyoyin agaji suka yi kan cewa babu isasshen tsaron soji a wuraren.