fidelitybank

Boko Haram sun kashe mutane 40 a jihar Yobe – Ƴan Sanda

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, ta ce wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun halaka aƙalla mutum 40 a jihar tsakanin ranakun Litinin da Talata.

Sun ce mayaƙan sun riƙa harbin mutane da bindiga da kuma jefa masu bam.

Ana ganin cewa wannan shi ne wani hari mafi muni da aka kai a jihar cikin wata 18.

Ƴan sintiri da ke aikin samar da tsaro a yankin sun ce mayaƙan na Boko Haram sun kai musu harin ne bayan da mazauna ƙauyukan suka ƙi biyan kuɗaɗen harajin da ƴan bindigar suka ƙaƙaba musu.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Yobe ya faɗa wa BBC Hausa cewa maharan sun fara kai hari ne ranar Talata tare da kashe gomman mutane a yankin ƙaramar hukumar Geidem.

‘Yan bindigar sun sake far wa masu zaman makoki a ranar Laraba, inda nan ma suka kashe mutane da yawa.

Ya ce har yanzu ba su kai ga tattara alƙaluman waɗanda aka kashe ba, amma mazauna yankin na cewa adadinsu ya kai kusan 40.

Sau da dama gungun ƴan bindiga a wasu ƙauyukan Najeriya kan nemi mazauna yankunan su biya haraji a wani yunƙuri na tabbatar da ikonsu.

vanguard newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp