Rundunar sojin ƙasar nan ta tabbatar da kisan dakarunta 22 tare da raunata wasu da dama a wani harin ƙunar baƙin wake da mayaƙan Boko Haram suka kai musu a jihar Borno.
Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran shalkwatar tsaron ƙasar, Manyo Janar Edward Buba ya fitar ranar Lahadi ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da sojojin suka ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin mayaƙan ƙungiyar da ke yankin Timbiktu a jihar.
Ya ƙara da cewa sojojin rundunar Operetion Haɗin Kai’, sun samu nasarar kakkaɓe ‘yantawayen masu yawan gaske a maɓoyarsu a wani hari da suka ƙaddamar musu – tun daga ranar 16 zuwa 25 ga watan Janairu – da nufin murƙushe su.
Manjo Janar Buba ya ce a lokacin harin kakkaɓe sansanonin mayaƙan, sojojin sun samu nasarar kashe mayaƙan ƙungiyar 70, cikin har da wasu manyan fitattun kwamandojin ƙungiyar uku.
”A lokacin kai harin, mayaƙan Boko haram ɗin sun girke abubuwan fashewa da ababen hawa da suka cika da abubuwan fashewa da ‘yan ƙunar baƙin wake domin dakatar da farmakin sojojin.
To sai dai ya ce kasancewar dakarun sojin sun saba da wannan dabara ta mayakan ƙungiyar, sun samu nasarar kauce wa yunƙurin na Boko Haram, ciki har da harbi da jirage marasa matuƙa.