fidelitybank

Boko Haram sun kashe jami’in Kwastam a cikin ofishin su na Yobe

Date:

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai hari ofishin hukumar kwastam da ke garin Geidam a karamar hukumar Geidam a jihar Yobe, inda suka kashe wani jami’in tsaro Usman Gombe.

A cewar wani rahoto, ‘yan ta’addan sun kai farmaki ofishin kwastam da ke kan titin Maine Soroa a cikin motar Golf Volkswagen da kuma wata mota kirar Land Rover da misalin karfe 10:00 na daren ranar Asabar, inda suka fara harbe-harbe.

“Sun kai hari lokacin da suka tabbatar da cewa jami’an Kwastam sun yi ritaya a gida. Cikin firgita da ruwan harsasai, jami’an sun yi ta tururuwa domin tsira da rayukansu; wasu sun tsere ta kofar gidan, yayin da wasu suka sike shingen.

“Abin takaici, an harbe daya daga cikin jami’an, Usman Gombe a lokacin da yake kokarin hawan katanga,” kamar yadda wata majiyar tsaro ta shaida wa Aminiya.

by TaboolaSponsored Links Kuna iya so
Auri ‘yar Kanada kuma Ka Yi Hijira Zuwa Kanada
Kanada IJ
Ya ce maharan sun kuma kona motar sintiri na hukumar Kwastam, da janareta, da wani bangare na ginin ofishin.

“Wannan shi ne karo na biyu da ‘yan Boko Haram ke kashe jami’an Kwastam. A watan da ya gabata mahara sun yi awon gaba da wani jami’i mai suna Babalola da karamin jami’insa, inda daga bisani maharan suka kashe shi,” inji majiyar.

Mazauna garin sun bayyana cewa ayyukan mayakan Boko Haram a wajen Geidam ya karu a ‘yan kwanakin nan.

“Suna karbar haraji daga manoma da makiyaya masu tazarar kilomita kadan daga garin, kuma babu wanda yake yin komai.

“Maimakon haka, jami’an tsaro sun sake tsugunar da shingayen binciken ababen hawa 17 cikin garin inda kuma suka rika biyan ‘yan kasuwar da ke shigo da kayayyaki ta wannan hanya haraji. Muna cikin tsaka mai wuya a wannan garin,” daya daga cikin ‘yan kasuwar ya yi zargin.

legit ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp