Rahotonni na cewa, mayaƙan Boko Haram sun kai hari kan wani sansanin soji a jihar Yobe.
Jaridun Najeriya sun ruwaito cewa ƴan bindigar sun ƙaddamar da hari kan sansanin soji na ”27 Task Force Brigade” da ke garin Buni Yadi, a yankin ƙaramar hukumar Gujba da tsakar daren Asabar.
Harin na zuwa ne kwana guda bayan ƙungiyar gwamnonin arewa maso gabashin ƙasar sun gudanar da taro a Tamaturu, babban birnin jihar da nufin magance matsalolin yankin, ciki har da matsalar tsaro.
A baya-bayan nan mayaƙan Boko Haram da na ISWAP na neman dawo da hare-hare a yankin.
A cikin makon nan ma ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin wani hari da yayi sanadin mutuwar mutum 26 a jihar Borno.