Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan ta’addar Boko Haram da mayakan kungiyar IS a yammacin Afirka sun kai hari a kan wani jirgin sama mai saukar ungulu a rundunar sojoji a jihar Borno a cikin makon da ya gabata.
Naija News ta samu labari cewa, ‘yan ta’addan da ake zargi da alaka da kungiyar Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah Wa’l-Jihād ne suka yi harbin kan wani jirgin sama mai saukar ungulu na rundunar hadin gwiwa ta MNJTF a ranar Alhamis a kokarin da suke yi na kai harin bam da shelikwafta.
Rundunar ta MNJTF wacce ta hada dakaru daga kasashen Benin da Kamaru da Chadi da Nijar da kuma Najeriya na cikin wani shiri lokacin da ‘yan ta’addan suka yi yunkurin tayar da bama-bamai.
Kungiyoyin tsaro dai na da shedikwatarsu a N’Djamena, kuma an dora musu alhakin kawo karshen ta’addancin Boko Haram a cikin wannan kundi.
An tsara rundunar a sassa hudu na kasa: Sector 1 (Cameroon) mai shedikwata a Mora; Sector 2 (Chad) mai shedikwata a Baga-Sola; Sashi na uku (Nigeria) dake garin Baga; da kuma Sector 4 (Niger), dake garin Diffa.
Rahotannin tsaro da aka samu daga Sahara Reporters sun nuna cewa, dan ta’addan ya yi amfani da nagartattun bindigogin kakkabo jiragen sama da kuma GPMG yayin harin da aka kai wa jirgin a ranar Alhamis din da ta gabata.