Rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF) da ke yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi ta ce, ‘yan ta’addar Boko Haram 263 da iyalansu sun mika wuya ga sojoji.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Lt.-Col. Abubakar Abdullahi, babban jami’in yada labaran soji na MNJTF a N’djamena, Chadi.
Ya ce maharan sun mika wuya ne tsakanin ranakun 11 ga watan Yuli zuwa 17 ga watan Yulin 2024, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin Operation Lake Sanity II.
“An fara mika wuya ne a ranar 1 ga watan Yuli, lokacin da ‘yan ta’adda biyar suka mika wuya ga dakarun MNJTF a Wulgo, da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.
“Bayanin farko sun nuna wadannan mutane sun fito ne daga Tumbuma da Kutumgulla a karamar hukumar Marte (LGA), Najeriya.
“A wannan rana, Malum Kori Bukar, mai shekaru 50, ya tsere daga maboyar Jibilaram, ya mika kansa ga sojoji.
“Bugu da kari, a ranar 11 ga watan Yuli, ‘yan ta’adda 19 sun mika wuya a kauyen Madaya da ke arewacin kasar Kamaru, sannan wasu 11 sun mika wuya a Wulgo daga maboyar Tumbuma cikin igiyoyi 2.
“A ranar 12 ga Yuli, 2024, mutane 64 sun mika wuya a Bonderi, Kamaru, ciki har da manya maza 6, mata 20, da yara 38. Moreso, a ranar 13 ga Yuli, ‘yan ta’adda 27 sun mika wuya,” in ji shi.
Ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa dukkan mutanen da suka mika wuya na al’ummar Najeriya ne.
“Saboda haka, an mika su ga dakarun Operation HADIN KAI domin ci gaba da daukar mataki,” in ji shi.