A yau ne Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken zai isa Najeriya a wani bangare na rangadin mako daya zuwa kasashen yammacin Afirka hudu.
Amurka na fafutukar ganin dorewar tasirinta yayin da take samun gogayya daga Rasha da China.
Kasashe a yammacin Afirka musamman a yankin Sahel sun fuskanci karuwar matsaloli ciki har da sauye-sauyen gwamnatoci a hudu cikin mambobin kungiyar ECOWA 15.
Ziyarar ta zo ne daidai lokacin da Abuja, babban birnin Najeriya ke fuskantar matsalolin tsaro da sace-sacen jama’a.
Najeriya ta fuskanci karuwar tashin hankali a arewaci da tsakiyar kasar inda yan bindiga ke kai hare-hare tare da satar mutane don kudin fansa.
Kungiyoyi masu ikirarin Jihadi kamar Boko Haram da sauran kungiyoyi masu tafka miyagun laifuka sun kashe daruruwan farar hula tare da daidaita fiye da mutum miliyan biyu a shekarun baya-bayan nan, wani lamari da ke sa shakku game da kokarin da gwamnatin Najeriya take ikirari na kawo sauye-sauye da magance matsalolin tattalin arziki saboda janye tallafin man fetur.
Shugaba Joe Biden na Amurka wanda ke fuskantar kalubale a kudurinsa na sake tsayawa takara, ya yi alkawarin kai ziyara Afirka bara sai dai hakan bai samu ba.
Rangadin da Blinken ke yi na iya zama cikin yunkurin cika alkawarin sai dai yana zuwa ne a lokacin da ake samun sauye-sauyen lamuran siyasa tun ziyararsa ta karshe zuwa yankin a farkon shekarar 2023.