fidelitybank

Biyu sun mutu Takwas sun jikkata a wani mumunan hadari a Sokoto – FRSC

Date:

Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Sokoto, Kaugama Kabo, ya tabbatar da mutuwar mutane biyu a wani hadarin mota da ya rutsa da motoci bakwai.

Kabo ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, a ranar Asabar cewa, hatsarin ya afku ne da sanyin safiyar Asabar a kauyen Sifawa da ke karamar hukumar Bodinga.

Ya ce, hatsarin ya rutsa da wata motar da ke tafiya inda ta rasa yadda za ta yi, ta kuma taba wasu motoci bakwai ciki har da manyan motoci biyu.

Kabi ya ce, hatsarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu yayin da wasu takwas suka samu raunuka daban-daban.

Ya kara da cewa, an kai wadanda suka mutu tare da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Bodinga.

Kwamandan Sashen ya gargadi direbobin da su guji yin gudu, tuki mai hatsari da sauran munanan halaye da ke jefa rayukan al’umma cikin hadari da lalata dukiyoyi.

nan news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp