Birtaniya da Amurka sun sanar da sake kakaba wa Hamas jerin takunkumai zagaye na uku tun bayan harin da ƙungiyar ta kai wa Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoba.
Baitulmalin Amurka wanda shi ne ma’aikatar harkokin kuɗin ƙasar na cewa takunkuman za su shafi “manyan kusoshin Hamas da kuma tsare-tsaren da Iran ke samar da tallafi ga Hamas da kuma ƙungiyar Islamic Jihad ta Falasɗinawa” – wadda ita ma wata ƙungiya ce mai gwagwarmaya da makamai a Zirin Gaza.
Kusoshin na fuskantar haramcin tafiye-tafiye da rufe kadarorinsu da kuma hana cinikayyar makamai.
Wasu daga cikin mutanen da takunkuman suka shafa akwai wakilin Islamic Jihad a ƙasar Iran, Naseer Abu Sharif da wani ɗan canji mazaunin Lebanon, wanda ake zargi da gudanar da harkokin tura kuɗi tsakanin Hamas da ƙasar Iran.


