fidelitybank

Birtaniya za ta haramta wa ɗalibai kai ƴan uwansu ƙasar

Date:

Birtaniya na shirin haramta wa ɗaliban ƙasar waje masu karatun digiri na biyu zuwa da ‘yan uwansu ƙasar, a yunƙurin gwamnati na rage yawan ‘yan ciranin da ke shiga ƙasar.

An fitar da sanarwar ne kwana biyu kafin alkaluman kididdiga a hukumance da ake sa ran za su nuna cewa waɗanda suka yi hijira zuwa ƙasar sun kai mutum 700,000 a wannan shekara.

A bara, an bai wa mutum 135,788 biza waɗanda ke karkashin kulawar ɗaliban ƙasashen waje, kusan ninki tara a kan adadin da aka bai wa a 2019.

Firaminista Rishi Sunak ya faɗa wa ministoci cewa matakin zai taimaka wajen rage masu ƙaura zuwa ƙasar.

Ya shaida wa majalisar ministocin cewa sauyin da zai fara aiki a watan Janairun 2024, zai taimaka “wajen rage yawan mutane da ke shiga ƙasar,” a cewar fadar gwamnatin Birtaniya.

A makon da ya gabata ya ce ministocin suna “la’akari da zaɓin da suke da shi” na rage yawan ƙaura, amma sun ƙi bayyana matakin da aka amince da shi.

A baya dai jam’iyyar Conservative ta yi alkawarin rage yawan mutanen da ke yin ƙaura zuwa Birtaniya zuwa ƙasa da mutum 100,000 a duk, amma ta yi watsi da manufar gabanin zaɓen 2019 bayan da ta ƙasa cimma burin.

Sanarwar ta ce ba za a sake barin ƴan uwa da kuma abokai na ɗalibai masu karatun digiri na biyu su nemi zama a Birtaniya ba yayin karatunsu, sai dai waɗanda ke karatu a kan kwasa-kwasan da aka keɓe a matsayin na bincike.

A shekarar da ta gabata, an bai wa waɗanda ke karkashin kulawar ɗaliban ƙasashen waje 135,788 biza, wanda ya kai sama da kashi biyar na duk bizar da aka bayar na tallafin karatu, idan aka kwatanta da kashi shida a shekara ta 2019.

Sakatariyar Harkokin Cikin Gida Suella Braverman ta ce ba a taɓa samun ƙaruwar mutanen da ke karkashin ɗaliban da ke karatu da ake bai wa biza ba kamar wannan lokaci,” kuma lokaci ya yi da za a ƙara tsaurara hakan wajen ganin an rage yawan bakin haure. In ji BBC.

A cikin wata sanarwa da ta aike wa majalisar, ta ƙara da cewa matakin zai “kawo daidaito” tsakanin rage ƙaura da “kare fa’idar tattalin arziki da ɗalibai za su iya kawowa Birtaniya”.

legit news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...
X whatsapp