Birtaniya ta fitar da sabon tsarin tisa keyar duk wani bako da aka samu da aikata laifi a ƙasar zuwa ƙasarsa ta asali.
Ministar shari’ar ƙasar, Shabana Mahmood, ta ce shirin tisa ƙeyar mutum gida zai rage asarar kuɗaɗen masu biyan haraji da dala dubu 70 da ake kashewa kowanne fursuna guda a shekara.
Kafin wannan lokaci duk wani bako da ke zama a Birtaniya da aka samu da laifi, a gidan yarin ƙasar ake ɗaure shi.
Sai dai waɗanda hukuncinsu ɗaurin rai da rai ne, da waɗanda suka aikata kisa ko ta’addanci – za su cigaba da kasancewa a ɗaure a Birtaniya bisa sabon tsarin.
Kashi 12 cikin 100 na fursunonin Birtaniya baki ne, kuma gwamnati na fuskantar matsin lambar rage cunkoso a gidajen yarin ƙasar.