fidelitybank

Birtaniya za ta dawo da kudin da James Ibori ya sace

Date:

Bayan bin tsare-tsare na sama da shekara 10, a yanzu gwamnatin Birtaniya ta kusan kammala ɗaukar matakan mayar wa Najeriya kuɗin da tsohon gwamnan jihar Delta James Ibori ya sace, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ta ruwaito.

Reuters ya ambato mai shigar da ƙara na Birtaniya na faɗa wa kotun cewa ƙasar za ta karɓo dala miliyan 129 daga hannun Mista Ibori.

A baya, masu shigar da ƙara sun ce James Ibori ya sace kimamin dala miliyan 165 daga jihar Delta mai arziƙin man fetur ta kudu maso kudancin Najeriya.

Shekara biyu da ta wuce ne, Birtaniya ta mayar wa Najeriya dala miliyan 5.8 da tsohon gwamnan ya sace.

A 2012 ne, aka tusa keyarsa daga Dubai zuwa Birtaniya, inda aka tuhume shi kan laifuka 10 da ke da alaƙa da zambar kuɗi. Bayan ya yi zaman gidan yari na wasu shekaru a Birtaniya, Ibori ya koma Najeriya a 2017.

A cikin wani gajeren saƙo da ya aike wa Reuters, Mista Ibori ya ce zai ɗaukaka ƙara kan umarnin ƙwace kuɗaɗen nasa da kotun ta bayar.

A ranar Juma’a ake sa ran fara mayar da kudin kamar yadda Reuters ya bayyana.

Birtaniya ta samu tsohon gwamnan da laifin satar kuɗaɗen tare da yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 13 a gidan yari a shekara ta 2012.

Tsohon gwamnan, ya amsa laifi a gaban kotun London, bisa jerin tuhume-tuhume goma da aka yi masa na haramta kuɗaɗen haram, da kuma haɗa baki domin tafka zamba.

Wannan ne karo na biyu da za a mayar wa Najeriya kuɗaɗen da tsohon gwamnan ya sace, bayan Birtaniya ta mayar wa Najeriya dala miliyan 5.8 a 2021 na almundahanar tsohon gwamnan.

A 2016, gwamnatocin Najeriya da Birtaniya suka sa hannun kan yarjejeniyar mayar da kuɗaden da masu laifi suka sace.

punch newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp