fidelitybank

Birtaniya ta tuhumi tsohuwar ministar man fetur ta Najeriya

Date:

Hukumar yaƙi da manyan laifuka a Birtaniya ta tuhumi tsohuwar ministar man fetur ta Najeriya a kotu, kan laifukan cin hanci.

Ana zargin Diezani Alison-Madueke da karɓar cin hancin miliyoyi barkatai na fam ɗin Ingila daga kwangilolin man fetur da iskar gas, da ta bayar don samun cin hanci.

Ranar 2 ga watan Oktoba, Diezani Madueke za ta bayyana a gaban Kotun Majistare ta Westminster.

Tun bayan kamun da aka yi mata na farko a London cikin watan Oktoban 2015, Diezani Alison-Madueke ta ci gaba da zama a matsayin beli.

Wata sanarwa da sashen yaƙi da cin hanci da rashawa na duniya a Hukumar Yaƙi da Manyan Laifuka ta Ƙasa ta ce ana zargin Diezani ta ci gajiyar aƙalla fam 100,000 kuɗi hannu, da samun zungura-zunguran motocin alfarma da ɗaukar jirgin sama na shata don tafiye-tafiye da tafiya hutun alfama da kuma kadarori birjik a London. In ji BBC.

Shugaban sashen yaƙi da cin hanci na ƙasashen duniya, Andy Kelly ya ce, “waɗannan tuhume-tuhume, muhimmin abu ne na wani cikakken bincike da sarƙaƙiya a cikin ƙasashen duniya.”

Diezani Alison-Madueke, ‘yar shekara 63, ta kasance a matsayin Shugabar Ƙungiyar ƙasashe Masu Arziƙin Man Fetur (OPEC), kuma ministar man fetur ta Najeriya a tsakanin 2010 zuwa 2015.

Hukumar yaƙi da manyan laifukan ta kuma fitar da bayanai dalla-dalla na ladan kuɗi da ta samu ciki har da kujerun gida da aikin gyaran fuska da ma’aikatan gidaje da ta samu, sannan an yi batun biyan kuɗin makarantar ‘ya’yanta da kyautuka daga kantuna masu sayar da kayan gayu na alfarma irinsu kantin sarƙoƙin yari na Cartier Jewellery da kayan gayu na kantin Louis Vuitton.

Tuni aka rufe kadarori na miliyoyin fam da ke da alaƙa da laifukan da ake zargi a wani ɓangare na binciken da ake ci gaba da yi, a cewar hukumomi.

A bara ne, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya ta ce ta ƙwace kuɗi sama da dala miliyan 153 da kadarori fiye da 80 daga hannun tsohuwar ministar ministar wadda aka yi imani tana zaune a London.

Ana alaƙanta ta da jerin zarge-zargen halasta kuɗin haram da karɓar cin hanci da batutuwan ƙwace kadarori a Najeriya da Italiya da kuma Amurka.

Ta yi aiki a matsayin minista daga shekara ta 2010 zuwa 2015, kuma ita ce mace ta farko da ta riƙe muƙamin ministar man fetur a Najeriya kuma ta farko da ta jagoranci ƙungiyar OPEC ta ƙasashe masu arziƙin man fetur a duniya.

Andy Kelly ya ce: “Muna zargin Diezani Alison-Madueke da tozarta muƙaminta a Najeriya kuma ta karɓi ladan kuɗi daga kwangilolin miliyoyi barkatai na fam ɗin Ingila da ta bayar.”

Yayin zantawa da wata jaridar Najeriya a cikin watan Nuwamban 2015, an ambato ta tana cewa: “Na ƙalubalanci kowa ya kawo hujjar cewa na saci kuɗin gwamnati ko na jama’a.

“Ban taɓa satar kuɗin Najeriya ba.”

bbc naija news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp