Birtaniya ta sanar da sabbin takunkumai kan mutum 12 da ke da kusanci da Vladimir Putin ciki har da tsohuwar matarsa da wadda ake kallo a matsayin budurwarsa a yanzu.
Ana zarginsu da ɓoye biliyoyin daloli a madadinsa. Hukumomin Birtaniya sun bayyana cewa kadarorin Mista Putin ba a cika rajistarsu da sunansa ba inda ake yawan saka su da sunan wasu.
Ciki har da wani jirgin ruwa na alfarma da ya kai dala miliyan 700 da wata kadara da ta wuce biliyoyi.
A hukumance, gwamnatin Rasha ta ce Mista Putin na da wani ƙaramin gida ne kawai a St Petersburg da wasu motoci na tun lokacin Tarayyar Soviet da kuma ƙaramin gareji