Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce, matakin da Birntaniy ta ɗauka na barazanar amincewa da ƙasar Falasɗinu tsantsar goyon baya ne ga ƙungiyar Hamas.
A ranar Talata ne, Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya bayyana cewa ƙasarsa za ta amince da kafa ƙasar Falasɗinu a watan Satumba, matuƙar Isra’ila ba ta dakatar da yaƙi da cika wasu sharuɗɗa ba.
Sai dai Netanyahu ya soki matakin da cewa tamkar nuna goyon baya ne ga abubuwan da Hamas ke yi.
”Starmer ya nuna wa munanan ayyukan Hamas goyin baya ta yadda za ta ci gaba da ayyukanta na ta’addanci da cutar da mutane”, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta
Matakin na Birtaniya ya yi kama da na Faransa, wadda ta ce za ta goyi bayan kafa ƙasar Falasɗinu a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya da za a yi a watan Satumba.
Shugaban Falasɗinawa, Mahmoud Abbas, ya yi maraba da wannan ci gaba, amma Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce hakan zai ƙarfafa Hamas ne kawai.
A halin yanzu dai, har yanzu ana fama da mummunar matsalar jin ƙai a Gaza, inda ake ci gaba da fafatawa.
Masana lafiya da Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce yunwa na ƙara tsananta a Gaza.
Yau ne rana ta ƙarshe ta taron kwanaki uku da Majalisar Ɗinkin Duniya ke yi, don neman mafita tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa.