Gwamnatin Birtaniya ta kori wani mai taimaka mata bayan ya nemi a tsagaita wuta a yaƙin da Isra’ila take yi a Zirin Gaza.
Fadar Downing Street ta ce Paul Bristow ya yi kalaman da “suka saɓa da aƙidar al’umma”.
Cikin wasiƙar da ya rubuta wa firaministan Birtaniya, Mista Bristow ya ce “tsagaita wuta mai ɗorewa” za ta ceto rayuka kuma ta ba da damar kai kayan agaji ga waɗanda suke buƙatarsa.
Gwamnatin ta Birtaniya na goyon “tsahirtawa saboda ayyukan jin-ƙai” amma ban da tsagaita wuta.
Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a makon da ya gabata, Firaminista Rishi Sunak ya ce “tsahirtawa saboda ayyukan jin-ƙai” za ta ba da damar shigar da agaji Gaza amma ya yi watsi da tsagaita wuta, yana cewa Isra’ila na da ‘yancin kare kanta.
Mista Bristow ɗan majalisar jam’iyyar Conservative ne daga mazaɓar Peterborough kuma mataimaki ne na musamman ga sakataren kimiyya da fasaha na Birtaniya.