Birtaniya ta janye wasu daga cikin ma’aikatan ofishin jakadancinta da ke Lebanon na wani ɗan lokaci da ‘yan uwansu sakamakon tashe-tashen hankula a yankin.
Ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta yi nuni da halin da ake ciki a yanzu a matsayin dalilin da ya sa aka dauki matakin.
Matakin na zuwa ne a dai dai lokacin da rikicin kan iyaka ya barke tsakanin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon da sojojin Isra’ila a cikin ‘yan makonnin nan.
Kafofin yaɗa labaran kasar Labanon sun rawaito cewa wani harin da Isra’ila ta kai a kudancin kasar ya yi sanadin mutuwar yara uku da kakarsu.
A martanin da kakakin sojin Isra’ila Daniel Hagari ya mayar, ya bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne biyo bayan harba makami mai linzami wanda ya yi sanadin mutuwar wani dan kasar Isra’ila