Wani dan Burtaniya ya gurfana gaban kotu a Landan kan zargin yi wa Rasha leken-asiri.
David Smith, wanda tsohon jami’in tsaro ne a ofishin jakadancin Burtaniya da ke Berlin, ya musanta tuhume-tuhume tara da aka gabatar a kansa, ciki har da bai wa wani jami’in Rasha a Berlin bayanan sirrin yakar makiya.
An mayar da shi gidan yari kafin ci gaba da sauraron ƙarar nan gaba. A cewar BBC.