Hukumar leƙen asirin Birtaniya MI5 ta ce, ta gano kusan ƴan ƙasar 10,000 da wasu masu leƙen asiri na ƙasashen waje ke bibiya ta hanyar amfani da shafukan bogi a Facebook da LinkedIn.
Masu leƙen asirin na bibiyar mutane a muhimman hukumomin gwamnati a kafofin sada zumunta suna tambayarsu wasu muhimman bayanai.
Wata sabuwar manhaja ta gwamnatin Birtaniya da ake kira The Think Before You Link na taimakawa mutane gano maso leƙen asiri na ƙasashen waje da ke fakewa a shafukan jabu a kafofin sadarwa na intanet. In ji BBC.
An samar da manhajar ne ga jami’an gwamnati da kuma waɗanda ke aiki a wasu muhimman wurare, amma kuma kowa na iya sauke manhajar.