An cin ma yarjejeniya tsakanin gwamnatin Birtaniya da Najeriya, wanda Birtaniya ta bayar da gudumuwar fam miliyan 10 a ƙasar.
Za dai a yi amfani da wadannan kuɗaɗen ne, domin a tabbatar da shirin COP26 da a ka shigo da shi Najeriya.
Baya ga haka, an sa hannu yarjejeniya a tsakanin juna na MoU da za su sa fam 210,000 su shigo cikin asusun Najeriya.
Thisday ta rawaito cewa, gwamnatin Ingila ta bada wadannan makudan kudi ne da nufin rage iskar carbon, sannan kuma a tabbatar a gyara wuta, a kuma goyi bayan shirin nan na COP26.