A ranar Talata ne kwamitin zartarwa na hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar Turai UEFA, ya tabbatar da cewa kasashen Ingila da Scotland da Ireland ta Arewa da Jamhuriyar Ireland da kuma Wales za su karbi bakuncin gasar EURO 2028.
Har ila yau, za a gudanar da gasar EURO 2032 a Italiya da Turkiyya.
An gudanar da bikin bayar da sanarwar ne a hedikwatar hukumar ta UEFA da ke birnin Nyon na kasar Switzerland.
Koyaya, bisa ga wani sakon da UEFA ta buga akan hannunta na X ranar Talata, “wuraren da aka gabatar sun hada da Belfast, Birmingham, Cardiff, Dublin, Glasgow, Liverpool, London (x2) Manchester da Newcastle.”
A halin yanzu, Jamus za ta karbi bakuncin EURO 2024.