Masana na ci gaba da tsokaci game da matakin shugaban ƙasa, Bola Tinubu na dakatar da ministar jin ƙai, Betta Edu da ake zargi da badaƙala daban-daban.
Matakin dakatarwar ya zo ne wata shida kacal da naɗa ta kan muƙamin minista kuma ita ce minista ta farko a karƙashin mulkin Tinubu da ta fuskanci suka kan zargin ta da almundahana.
Dr Abubakar Kari, wani masanin harkokin siyasa a Najeriya ya shaida wa BBC cewa matakin ya zo kan gaɓa kasancewa ya zo ne a daidai lokacin da al’ummar ƙasar ke kiraye-kiraye na a ɗauki mataki kan ministar da ake yi wa zargin almundahana.
Sai dai ya yi shakku kan ko gwamnati za ta iya ɗaukan mataki a kan ministar.
A cewarsa, matakin kuma zai bai wa gwamnatin Tinubu dama ta gudanar da bincike kasancewa gwamnatin na dabaibaye da zarge-zarge da batutuwa da dama.
Ya kara da cewa hanzarin dakatar da ministar zai aika saƙo ga jami’an gwamnati saboda watakila hakan ya sa su yi tunanin gwamnatin ta sha banban da gwamnatin da ta gada.
Dr Kari ya ce “duk da gwamnati ta bayar da umarnin a yi bincike a tura ta hukumar EFCC sannan ta kafa kwamiti a karƙashin ministan harkokin tsaro, amma bisa abubuwan da suke faruwa a baya muna da shakku cewa ba kawai suna neman lokaci ba ne maganar ta bi ruwa.”
Ya bayyana cewa matuƙar gwamnati ta yi bincike, to za a gano abubuwa da dama kuma hakan ne zai tabbatar wa ƴan Najeriya ko da gaske ita gwamnatin Tinubu take ko kuma “kawai ta yi ne domin ta sama wa kanta lokaci da kuma sarari.”
Masanin siyasar ya ce zai yi wuya ministar ta koma kan kujerarta ko da kuwa an wanke ta daga zarge-zargen da ake mata, idan kuwa hakan ta faru, toh zai zama na farko a tarihi.
“Tun da ban taɓa jin akwai inda aka yi waɗannan manya-manyan zarge-zarge a jami’an gwamnati aka cire su kuma aka dawo da su ba.” in ji masanin.
Ya ƙara da cewa abu ne mai wahala a iya wanke ministar daga girman zarge-zargen da ake mata saboda “kusan kowane wayewar gari sai an ɓallo wani abu daga cikin abubuwan da ke faruwa a wannan ma’aikata tata wanda kuma akwai sunanta.” In ji BBC.


