Tana dai neman Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ne ta yi fassarar doka game da matakin da hukumar zaɓe ta ɗauka ranar 16 ga watan Afrilu, bayan an ayyana cewa ita ce ta yi nasarar zama gwamna, a zaɓen 18 ga watan Maris da kuma na cike-giɓi a ranar 15 ga watan Afrilu.
‘Yar takarar tana kuma neman kotu ta ba da umarni sannan ta hana INEC da jami’anta ɗaukar ƙarin wasu matakai na bayyana wanda ya yi nasara a zaɓukan da aka yi, har sai kotun ta yanke hukunci a kan buƙatar yin tsokacin shari’ar.
Mallam Ahmed Sajo, jami’i a kwamitin yaƙin neman zaɓe Sanata Aisha Binani ya shaida wa BBC cewa sun je kotu ne don a yi musu fassarar sashe na 149 na dokar zaɓe ta 2022.
“Sai an mata fassarar ma’anar dokar nan ta zaɓe, sashen da ya ce idan an rigaan ayyana ɗan takara ya ci zaɓe, to sai kotu ce kawai za ta iya warware wannan ayyanawar, ba hukumar zaɓe ko wani mutum ba” in ji Mallam Sajo.
Don haka ƙara na neman kotu ta dakatar da hukumar zaɓe yin duk wani abu har sai ta kammala wannan aiki.