Rundunar tsaro ta NSCDC, reshen jihar Yobe, ta tura jami’anta 862 domin tabbatar da gudanar da bukukuwan karamar Sallah babu cikas a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Bala Garba ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Lahadi a Damaturu.
Garba ya ce kwamandan jihar, Adamu Zakari, ya bayar da umarnin tura jami’an a kananan hukumomi 17 na jihar gabanin bikin Sallah.
“An zabo jami’an ne daga Rundunar Mata, FSF, Counter Terrorist Squad (CTS), Rapid Response Squad (RRS), Anti Vandal Department, Intelligence and Investigations (INTs), Agro Rangers da Operations sashen,” Garba ya bayyana.
Ya kara da cewa an umarce su da su kasance masu himma tare da mutunta mutane yayin gudanar da ayyukansu.
A yayin da ya yaba wa al’ummar jihar kan yadda suka kasance masu bin doka da oda, ya taya daukacin al’ummar musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan da kuma bukukuwan Sallah lafiya a gaba.
Ya kuma bukace su da su kai rahoton duk wani motsi na mutane ko wani abu da suka yi kama da su ga hukumar tsaro mafi kusa.