Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya kai wa magabacinsa, Sanata Ahmed Lawan ziyarar Sallah a gidansa da ke Abuja ranar Juma’a.
Ziyarar dai ta kasance domin taya tsohon dan kasa mai lamba uku murnar zagayowar bukukuwan karamar Sallah da kuma tattaunawa mai ma’ana, tare da mai da hankali kan ci gaban majalisar dattijai da kuma kudurin da ta dauka na samar da ribar dimokuradiyya ga ‘yan Najeriya.
Ziyarar wacce aka gudanar cikin yanayi mai dadi, ta kuma yi zaman addu’a, kafin a yi tattaunawar sirri da nufin farfado da dimokradiyyar Najeriya.
Sanata Akpabio ya tabbatar wa Lawan cewa, gwamnatinsa za ta kasance cikin hadaka, ba tare da la’akari da bangaranci, kabila, ko addini ba.