fidelitybank

Bieber ya sayar da hakkin mallakar wakokinsa dala miliyan 200

Date:

Justin Bieber ya sayar da wani bangare na hakkin mallakar waƙoƙinsa ga kamfanin waƙoƙi na Hipgnosis Songs Capital kan kudin dala miliyan 200.

Yanzu kamfanin ne ke da hakkin mallakar wasu daga cikin waƙoƙin Justin na baya-bayan nan – ciki har da waƙar “Baby” da “Sorry”.

Wannan mataki na nufin kamfanin Hipgnosis zai rika karɓar kudaden sauraren duk wata waƙa da aka saurara a bainar jama’a ta mawakin.

Kamfanin ke da hakkin wallafa wakokin Justin Bieber da suke faifansa mai dauke da waƙoƙi 290.

Wannan ya haɗa da suka waƙoƙinsa da mawallafinsa ya saki gabanin ranar 31 ga watan Disambar 2021.

Babban hakkin mallakar tsarin naɗar waƙoƙin mawaƙin shi ma na cikin wannan tsari.

Kamfanin Hipgnosis bai bayyana sharudan da aka cimma ba a kwantaragin, amma wata majiya ta bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa darajar kwantaragin ta kai ta dala miliyan 200.

Ana samun ƙaruwar mawakan da ke sayar da haƙƙin mallakarsu ga kamfanonin kiɗe-kiɗe – ciki har da Justin Timberlake da Shakira, waɗanda suma suka cimma yarjejeniyar kwantaragi da kamfanin Hipgnosis.

www.legitnews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp