fidelitybank

Bidiyon kisan Filato da ake yadawa karya ne – Sojoji

Date:

Rundunar Sojin Najeriya ta musanta rahotonnin da ake yaɗawa tare da wani bidiyo a shafukan zumunta cewa dakarunta ne ke wulaƙanta wasu mata a jihar Filtao da ke tsakiyar ƙasar bayan hare-haren ‘yan bindiga.

Rundunar ta ce bidiyon na ɗauke da kanun “Operation Rainbow in Plateau State”, inda a ciki aka ga wasu sojoji na cin zarafin wasu mata.

Wata sanarwa da Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar ta tabbatar da cewa sojojin Najeriya ne a bidiyon amma ba a Filato abin ya faru ba kamar yadda wasu ke yaɗawa.

“Haƙiƙanin gaskiya lamarin ya faru ne a Dajin Sambisa a 2021, kuma matan wasu ne daga cikin abokan zaman mayaƙan Boko Haram a lokacin da aka kama wasu daga cikin garuruwansu,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa tuni rundunar ta bincike kuma “ta hukunta waɗanda suka aikata hakan saboda nuna rashin ƙwarewar aiki”.

Wasu daga cikin masu yaɗa bidiyon na nuna cewa lamarin ya faru ne a yankunan Bokkos da Barkin Ladi na jihar Filato bayan ‘yan bindiga sun kai hare-hare tare da kashe mutum kusan 200 lokacin bikin Kirsimeti.

“Muna kira ga masu sake yaɗa wannan bidiyo da su daina yin hakan saboda yana ƙara ta’azzara ƙalubalen tsaron da ake ciki wanda kuma rundunar Operation Safe Heaven ke ƙoƙarin daƙilewa,” a cewar sanarwar.

bbc naija news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp