Shugaba Biden zai kai ziyara Isra’ila a gobe Laraba, a wani ɓangare na nuna goyon baya ga ƙasar a yayin da ta ke ci gaba da yaƙi da Hamas.
Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ne ya sanar da ziyarar shugaban bayan wata tattaunawa cikin dare da suka yi a Tel Aviv.
Ya ce za a faɗa wa shugaban irin dabarun da Isra’ila ke amfani da su, da kuma yadda za a takaita hare haren da ake kai wa kan fararen hula.
Mr Blinken ya kuma ce shugabannin Isra’ila sun amince a samar da wani tsari da zai bay


