Shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden ya jagoranci suka da Allah-wadaran da kasashen duniya ke yi kan harin makami mai linzamin da aka kai kan wata tashar jirgin kasa a gabashin Ukraine, harin da ya hallaka farar hula sama da hamsin.
Wannan dai na zuwa ne, yayin da jami’an kasashen Yamma ke cewa, Rasha ta sake tsarin shugabacin sojinta a Ukraine, inda ta sanya wani janar a wanda ya jagoranci dakarun Rasha a yakin Syria, a kan shugabancin.
Shugaba Biden ya bi sahun masu zargi da sukar Rasha da kai harin cewa, ta kai wannan mummunan hari ne na tsabagen mugunta, a lokacin da ta harba makami mai linzamin kan tashar jirgin kasan a Gabashin Ukraine, a lokacin da take makare da fararen hula, inda ta kashe mutane akalla hamsin.
Wadanda harin ya rutsa da su a tashar wadda a lokacin dandazon mutanen ya kai dubu hudu, yawancinsu mata ne da kananan yara da tsofaffi, wadanda ke shirin tserewa daga tsammanin zuwan dakarun Rasha da ke durfafar yankin Gabashin Donbas.