Shugaba Joe Biden ya yi wani jawabi ga al’ummar Amurka, inda a ciki ya yi kakkausar suka ga jiga-jigan jam’iyyar Republican ciki har da tsohon Shugaba Donald Trump.
Ya soki taken akidarsu da cewa barazana ce ga Amurkawa. A jawabin nasa na Philadelphia, Mr Biden ya ce tashin hankali ba shi da wuri a siyasar Amurka, akan haka ya bukaci al’umma da su zo a hada hannu don kawar da aabinda ya kira mummunar akidar yan Republican.
Ya ce ina so in sanar ƙarara cewa tashin hankali mai nasaba da siyasa ba shi da wuri a Amurka. In ji BBC.
Tun da farko Mr Trump ne ya ce idan har ya sake cin zabe zai yi afuwa ga wadanda ake tsare da su, da laifin kutsawa Majalisar kasar a watan Janairun bara.