fidelitybank

Biden ya shiga tsaka mai wuya bayan majalisar Amurka ta yi yunƙurin tsige shi

Date:

Shugaban Majalisar Wakilan Amurka, ya ce, Majalisar za ta ƙaddamar da bincike kan batun tsige shugaba Joe Biden a hukumance.

Kevin McCarthy ya ce, binciken zai mayar da hankali ne kan zarge-zargen “saɓa ƙa’idar aiki, kawo cikas wurin aiki da kuma rashawa.”

Ƴan majalisa na jam’iyyar Republican sun kwashe lokaci suna bincike kan Biden, tun bayan da suka ƙwace iko da zauren majalisar a watan Janairu.

Ba a dai samu Biden da wani laifi ba takamaimai tun bayan fara bincike-binciken.

Wannan ne mataki na farko a tsarin da za a bi wanda zai iya kai ga batun kaɗa ƙuri’a kan tsige shugaban a Majalisar Wakilai ta ƙasar.

A wani saƙo da ya fitar a ginin majalisa na Capitol, Mr McCarthy ya ce “akwai ƙwararan hujjoji kan zarge-zargen da ake yi wa shugaban ƙasar.”

Yanzu haka dai ana binciken ɗan shugaban ƙasar, Hunter Biden, bisa zargin saɓa wa dokar biyan haraji a harkar kasuwancinsa.

nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp