Shugaba Joe Biden na Amurka ya kai wata ƙwarya-ƙwaryar ziyara zuwa iyakar ƙasar da Mexico a wani yunƙuri na daƙile sukar da ake yi wa tsare-tsarensa kan baƙin da ke shiga ƙasar.
Ita ce ziyararsa ta farko zuwa kan iyakar tun bayan da ya hau kan karaga shekaru biyu da suka gabata.
Mista Biden ya leka wata mashiga mai cike da cunkoson jama’a a birnin El Paso da ke Texas inda ya yi tafiya ta jikin shingen ƙarfen da ya raba ƙasashen biyu.
Ƴan jam’iyyar Republicans sun ce Mista Biden bai taka wata rawar a zo a gani ba wajen daƙile kwararar baƙi ta haramtacciyar hanya a Amurka.
Gwamnan Texas, Greg Abbott ya zarge shi da haifar da hargitsi. Yanzu dai mista Biden ya tafi Mexico domin halartar wani taron shugabannin ƙasashen Amurka ta Arewa.
Gwamnan Texas ke cewa ya kamata Biden yatashi haiƙanwajen ɗaukan mataki cikin gaggawa tare da mayar wa Texas kuɗaɗen da ta kashe amma samar da kayan aikin da suka kamata domin gwamnatin tarayya ta aiwatar da ayyukan da suka rataya a wuyanta.