Shugaba Joe Biden ya tattauna ta wayar tarho tare da firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, da kuma shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas.
Mista Biden ya bukaci Isra’ila da ta samar da kariya ga Falasdinawa fararen hula.
shugaban na Amurka ya kuma bukaci Mista Abbas da ya fito ya yi Alla-wadai da abin da Hamas ke yi.
Nan gaba a yau ne kuma sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, zai kai ziyara Masar, a wani ɓangare na rangadin da yake yi a ƙasashen Larabawa da nufin kare bazuwar rikicin.
Mista Blinken ya mayar da hankali sosai da sosai a kan halin da jama’a ke ciki a Gaza a yayin da ya nuna damuwa a kan yadda rikicin ya rincaÉ“e.